IQNA

Muftin Kasar Masar: ‘Yan Ta’adda Masu Da'awar Jihadi Suna Canja Ma’anonin  Ayoyin Kur’ani Da Sirar Ma’aiki (SAW)

22:59 - May 30, 2021
Lambar Labari: 3485965
Tehran (IQNA) Muftin kasar Masar ya bayyana cewa ‘yan ta’adda suna birkita ma’anonin ayoyin kur’ani.

Shafin yada labarai na Misri Alyaum  ya bayar darahoton cewa, a cikin wani shiri a gidan rediyon Sadal balad, babban mai bayar da fatawa na kasar Masar Shauki Allam ya bayyana cewa ‘yan ta’adda suna karkatar da ma’anonin ayoyin kur’ani da kuma sirar manzon Allah (SAW) wajen yin amfani da hakan domin ayyukan ta’addanci da sunan addini.

Ya ce suna kafirta musulmi sanann su halasta jininsu, ta hanyar murguda ma’anonin ayoyin kur’ani mai tsarki, da kuma jahilcinsu a kan addininin muslunci da hakikanin koyarwarsa.

Ya ce dukkaniun abin da suke yi bai doru a ka wani dalili na addini ba, domin kuwa karkatar da ma’anoni na addini sabnanin abin da addini yake nufi, domin ko a lokacin manzon Allah (SAW) jihadi yana da matakai da sharudda, da kuma mutanen da ake yaka.

Malamin ya ce, dukkanin yake-yaken muslunci sun zo ne domin kariyar kai daga cutarwar mushrikai da sauran makiya musulunci, bisa sharudda na jihadi,sabanin abin da ‘yan ta’adda suke yi a yanzu da sunan jihadi, suna bata wa muslunci suna, domin kuwa jihadi lamari ne mai muhimmanci da girma  da matsayi na musamman a cikin msulucni, bata ma’anar jihadi, ba ta sunan addinin muslunci ne.

3974476

 

 

 

captcha